3 Yuli 2026 - 22:03
Source: ABNA24
Hizbullah Na Lebanon Za Ta Gudanar Da Taron Tunawa Da Shahidin Jagoran Juyin Juya Hali A Dahieh Beirut

Ƙungiyar Hizbullah ta Lebanon ta sanar da shirya bikin tunawa da jagora shahidin juyin juya halin Musulunci a Dahieh ta kudancin Beirut, kuma ta buƙaci jama'ar Lebanon su halarci wannan bikin da za a gudanar da yammacin ranar Laraba mai zuwa.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya bayar da rahoton cewa: Ƙungiyar Hizbullah ta Lebanon ta buƙaci jama'ar Lebanon su halarci taron tunawa da shahidin jagora shahidin juyin juya hali da za a gudanar. Ana sa ran gudanar da wannan taro da yammacin ranar Laraba mai zuwa da karfe 21 na agogon gida, a Dahieh Beirut.

Da safiyar yau Juma'a, a daidai lokacin da ake shigowa da gawar jagora shahidin juyin juya halin Musulunci zuwa filin sallah na Imam Khomeini (R.A) a Tehran, wasu gungun shugabannin siyasa, malamai, masana da kuma shugabannin addinai daga kasashe daban-daban na duniya, ta hanyar kasancewa a wannan taron, sun yi  gaisuwar girmamawa ga gawarsa mai tsarki.

A wannan Taron, kwamitoci daga shugabannin siyasa, malamai da masana addini daga kasashen India, Rasha, Pakistan, Norway, Sri Lanka, Ingila, Cambodia, Girka, Sweden, Myanmar da Thailand, Indonesia, Afghanistan da sauran kasashe, ta hanyar kasancewa kusa da gawar jagora shahidin juyin juya hali, sun karanta suratul Fatiha da nuna juyayi, sun kuma girmama tunawa da gwagwarmayar da ya yi don kare al'ummar Musulunci da kuma goyon bayan al'ummomin da ake zalunta.

………………………

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha